Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya amince da biyan albashin watan Yuni nan take ga ma’aikatan jihar da kananan hukumomi da kuma malamai kazalika da yan fansho.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawun gwamnan jihar Sokoto Malam Abubakar Bawa
Sanarwar tace wannan yunkurin dai nada manufar ganin ma’aikatan jiha sun samu sukunin gudanar da sallah Babba a cikin walwala.
Gwamnan ya kara jaddada aniyar gwamnatin sa na ganin ta kyautatawa ma’aikata tare Kuma da farfadowa da darajar aikin gwamnati. Haka kuma, ya bukaci ma’aikatan dasu sakawa wannan yunkurin ta hanyar zamowa masu gaskiya,tsare aiki da kuma zuwa aiki cikin lokaci
Gwamna ahmad Aliyu ya kuma roki alummar jihar Sokoto dasu ci gaba da yiwa Gwamnati addua don samun nasarar biyan bukatun jama’a