Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya hadu tare da sauran shugabannin kasashen duniya a birnin Paris ta kasar France a wajen babban taron kan yarjejeniyar kwaskwarima ga tsarin hada-hadar kudi na duniya, wacce kai tsaye hakan zai taimaka wajen rage kaifin talauci, shawo kan basuka ko sokewa da kuma la’akari da kananun kasashen da annobar Korona ta raunata.
Tinubu ya halarci wurin taron da ke Palais Brongniart, da karfe 8.59 am agogon Nijeriya domin halartar bude taron sabon tsarin hada-hadar kudi na duniya, inda ya samu tarba daga ministan Faransa da ke kula da harkokin kasashen waje, Catherine Colonna.
A sanarwar manema labarai, Dele Alake, da yake maraba da bakin, shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya ce, babban taron na da manufar hada tunani waje guda ne domin samar da sabon tsarin hada-hadar kudi na duniya wanda hakan zai taimaka wa kasashe masu tasowa wajen sauyin makamashi, yaki da talauci da fatara, tare da muunta ‘yancin kowace qasa domin kyautata rayuwa.