955
Yan Najeriya na ci gaba da kokawa akan illolin da matsalar rashin tsaro ke ci gaba da haifarwa wadanda ke kara durkusar da kasar da jama’ar ta.
Wannan na zuwa ne lokacin da ‘yan bindiga ke ci gaba da kisa da garkuwa da manoma, yayin da wasu jama’a suka shafe shekaru zaune ba abin yi saboda matsalar ta rashin tsaro.
Matsalar rashin tsaro dai ta jima tana kawo koma baya a Najeriya musamman a jihohin arewa.