Rundunar sojin Najeriya ta ce ta damu da yadda ayyukan ‘yan ta’adda ke sake kunno kai a wasu yankuna, kuma ba za ta yarda a ci gaba da salwantar da rayukan jama’a tana kallo ba.
Wannan na zuwa ne lokacin da rundunar ta ke samun ƙwarin gwuiwa daga wasu gwamnatoci a ƙoƙarinta na samar da tsaro a Najeriya.
ihar Sakkwato na daga cikin wuraren da ‘yan bindigar suke kai hari ga jama’a, inda a kasa da mako daya an sami kai hare-hare da satar mutane a yankuna da suka hada da Kware, Illela, Gwadabawa, Sabon Birni, Wurno da Isa inda jama’a ke ta kokawa.
Ɓullar matsalar tsaro a Ƙaramar hukumar Tangaza ne ya sa rundunar sojin Najeriya lasar takobin kawo ƙarshen kisan gillar da ake yi wa jama’a.
Mai magana da yawun gwamnan Sakkwato Abubakar Bawa wanda ya fitar da wata sanarwa bayan kammala taron gaugawa da gwamnan ya gudanar tare da hukumomin tsaron, ya ce “tsarin da gwamnati ta yi ya bambanta da na gwamnatoci da suka gabata, saboda wannan gwamnati tana da azamar ganin an kawar da rashin tsaro
“A taron da gwamna ya yi da hukumomin tsaro an gano wasu matsaloli da ke kawo koma baya ga ayyukan jami’an tsaro da suka hada da rashin biyan su kudaden alawus har tsawon wata biyar, kuma motocin da suke aiki da su suna cikin mummunan yanayi.
Inda gwamnatin ta dauki matakan gyara ga wadannan matsalolin domin daga wannan wata na Yuni za a cigaba da biyan kudin alawus ga zaratan jami’an tsaro dake bakin daga.
Matsalar rashin tsaro ta jima tana addabar jama’a a Najeriya duk da kokarin da gwamnatocin da suka shude da kuma iƙirarin da suke na shawo kan matsalar.
Abin jira dai a gani shi ne yadda sabbin gwamnatoci za su ɓullo da wata hanya da zai kawo ƙarshen matsalolin rashin tsaro.