Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar aiki ga babban sakataren Asusun Tallafa wa Manyan Makarantu na Ƙasa, TETFUND, Arc. Sonny Econo da sauran ma’aikatansa a Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Gwamnan ya bayyana cewa ziyarar ta sami tagomashi sosai duba da cewa an tattauna batutuwa da dama waɗanda za su sa a sami haɗin guiwa a tsakanin TETFUND ɗin da kuma Gwamnatin Kano domin tallafa wa ci gaban manyan makarantun jihar Kanon.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita.