Wata kungiya mai rajin yaki da cin hanci da rashawa, Movement Against Corruption in Nigeria (MACIN), ta yi kira ga ‘yansandan kasa da kasa na Interpol da hukumar lura da shige da fice ta ƙasar nan, su sanya ido kan tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje domin kada ya tsere sakamakon binciken da ake masa kan zargin cin hanci.
A yayin wani taron manema labarai da jagoran kungiyar, kwamared Kabiru Sa’idu Dakata ya gabatar, ya nemi hukumomin su Sanya wa tsohon gwamnan ido, domin shirin ficewa da yake zuwa ketare bayan da hukumar yaki da cin hanci ta Kano, ta nemi ya bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi kan faifan bidiyon Dalar.
Dakata, ya shawarci tsohon gwamnan da ya amsa gayyatar hukumar domin gaskiya ta yi halinta, ko dai a wanke shi daga zargin ko kuma ya amsa laifinsa.
Kazalika, kungiyar ta yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da kada ya bada dama a lullube mutanen da ake zargi da cin hanci a gwamnatinsa.
Ana dai zargin Ganduje da karbar kudi da aka ce sun kai Dala miliyan biyar na cin hanci lokacin yana kan gwamnan jihar.
Tuni dai hukumar yaki da cin hanci ta Jihar Kano ta dawo da aikin binciken, bayan da kwararru suka tabbatar mata da cewar bidiyon na da sahihanci.