Gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya naɗa Alhaji Sani Abdulkadir Dambo a matsayin sabon shugaban hukumar tattara haraji ta jiha wato KIRS.
Hakan na ƙunsha ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga shafin Sakataren yada labaran Gwamnan jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofainda ya bayyan cewar, shugaban na hukumar harajin, na cikin kungiyar malaman haraji na kasa, kuma ya fi shekara 20 ya na irin wannan aiki.
Kafin yanzu ya rike wannan mukami a baya, sannan yanzu haka Sani Abdulkadir Dambo babban jami’i mai binciken haraji ne a hukumar tattara haraji ta kasa. A yammacin Alhamis ne dai aka ji cewa, Alhaji Isyaku Abdullahi Kubarachi ya zama sabon shugaban hukumar SEMA mai bada agajin gaggawa. inda Isyaku Abdullahi Kubarachi da Dambo za su fara aiki daga yau Juma’a, 16 ga watan Yuni 2023.