Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da Shugaban Kwalejin Lafiya ta Health Technology, Bello Ɗalhatu, da Mai riƙon Shugabancin Hukumar Lura da Makarantun Sakandire ta jiha KSSMB, Malam Ado Tumfafi.
Wata sanarwa da Sakataren Gwamnati jiha Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya fitar, ta bayyana cewa an dakatar da su ne saboda zargin karɓar kuɗaɗe daga ɗalibai da kuma wasu zarge-zarge na danban.
Sanarwar ta zargi Tumfafi da karɓar kuɗin ɗalibai da sanya wa malamai haraji da sunan kuɗin fom ɗin ƙarin girma da sauransu.
Gwamnatin ta kuma umarci manyan sakatarorin ma’aikatun ilimi da lafiya da su kafa kwamitin bincike a kan mutan biyu.
Gwamnatin Kano ta ce ba zata sassauta wa duk wani shugaban hukuma da ya yi amfani da ofishinsa wajen muzgunawa jama’a ba.
Haka kuma ta yi alƙawarin ƙwato wa iyayen ɗalibai da Malaman da aka karɓi kuɗaɗansu haƙƙoƙinsu.