Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Yan kwamitin riko na hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars (Masu Gida).

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran Gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya raba wa manema labarai.

