Home » Rundunar ‘Yan Sanda Sun Raba Wa Iyalai da ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukansu Naira miliyan 23,574,204

Rundunar ‘Yan Sanda Sun Raba Wa Iyalai da ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukansu Naira miliyan 23,574,204

by Anas Dansalma
0 comment
Rundunar 'Yan Sanda Sun Raba Wa Iyalai da 'yan uwan wadanda suka rasa rayukansu Naira miliyan 23,574,204

Kwamishinan ‘yansandan Jihar Zamfara, Muhammad Bunu, a madadin babban sufeton ‘yansanda na kasa, Usman Alkali Baba ya gabatar da check ɗin kudi na Naira miliyan 23,574,204 ga iyalai da ‘yan uwa 21 na jami’an ‘yansanda da suka rasa rayukansu a bakin aiki.

Kakakin ‘yansandan Jihar, ASP Yazid Abubakar, ya bayyana haka a takardar da ya sa wa hannu ga manema labarai a Gusau.

A cewarsa, Kwamishina Bunu, a lokacin da yake gabatar da check ɗin kudin, ya yaba wa Sufeton ‘yansandan bisa irin wannan karimcin da ya nuna, sannan kuma ya bukaci iyalan jami’an da suka mutu da su yi amfani da kudaden wajen kula da iyalansu cikin adalci.

Abdulrahman Ahmed, daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin a jawabinsa a madadin sauran wadanda suka amfana, ya mika godiyarsa ga Sufeto Janar na ‘yansanda da kuma rundunar ‘yansanda bisa tallafin da suka ba su, ya kuma ba da tabbacin cewa za a kashe kudaden da aka ba su ta hanyar da ta dace.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?