Gwamnatin Kano ta shawarci al’umma da su kwantar da hankalinsu kuma su guji yin duk abin da zai iya zama saɓa wa doka.
A yammacin jiya Alhamis, wata majiya ta ce Kwamishinan yada labarai na Kano, Alhaji Baba Halilu Dantiye ya yi wannan kira a wani jawabi da ya fitar, inda ya ce shawarar ta zama dole ne ganin cewa wasu bata-gari za su iya amfani da damar shari’ar zabe, su kawo rikici a Kano.
A cewar kwamishinan, akwai buƙatar a zauna lafiya domin cigaban jihar Kano da kuma daukacin kasa. Daga nan ya yi kira ga jami’an tsaro da su ƙara ƙoƙari wajen ganin sun tabbatar da zaman lafiya da aminci.