Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ya ayyana Litinin 2 ga watan Oktoba a matsayin hutu a faɗin ƙasar nan domin tunawa da cikar Najeriya shekaru 63 da samun ‘Yancin Kai.
Ministan, a cikin jawabin nasa, ya ba wa al’ummar ƙasar ƙarin tabbacin game da ƙoƙarin da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu take yi na magance matsalolin da ƙasar nan ke fama da shi.
Inda ya jaddada muhimmancin haɗin kan ‘yan Najeriya wajen ciyar da ƙasar nan gaba.
Ya ce la’akari da yawan al’umma da arziƙin da Najeriya ke da shi wata manuniya ce kan irin matsayin da ƙasar nan ke da shi a Afirka, inda ya nanata muhimmancin jingine bambancin addini da ƙabilanci wajen haɗa kai domin ɗaga darajar ƙasar nan.