Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci dukkan kwamishinoni da ya naɗa da su hanzarta yin biyayya ga dokoki da ƙa’idojin aiki wanda suka zama tilas.
Inda yaƙara da cewar, daga yanzu, duk wanda ya san sunansa ya shiga cikin waɗanda za’a naɗa kwamishina ya bayyana dukiyar da ya mallaka gabanin majalisa ta tantance shi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wata gajeruwar sanarwa da gwamnatin Kano ta fitar a yau Laraba, inda gwamnan ya sha alwashin cewa duk kwamishinan da ya kauce wa cike Fam din bayyana dukiya daga hukumar kula da ƙa’idojin aiki, ba zai rantsar da shi ba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudurinsa ga al’ummar jihar Kano, inda ya ce, gaskiya da kiyaye haƙƙin sauke nauyi ne zasu zama alkiblar gwamnatinsa.
A cewarsa, ta haka ne kaɗai zai cika alkawarin da ya ɗauka a kakar zaɓe da kuma abinda ke cikin kundin manufofinsa na kafa nagartacciyar gwamnati da kowa zai yi na’am da ita.