Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda ya gabatar da ƙudirin kasafin kudin shekarar 2026 mai kimanin Naira biliyan 897.9 ga majalisar dokokin jihar.
Ya bayyana hakan ne a shafinsa na X, inda ya bayyana cewa kasafin kudin na bana shi ne mafi shiryawa tare da shigar da ra’ayoyin jama’a fiye da kowane lokaci a tarihin jihar.
A cewar gwamnan, an kasafin laƙabi da taken “Gina Makomarku III” domin ya nuna yadda aka gina shi ne kan bukatun al’umma da suka fito kai tsaye daga ƙananan hukumomi da mazaɓu
Ya ce sama da mutum 71,000 daga mazabu 316 ne suka bayar da gudummawa ta hanyar bada shawara da bukatun da suka ke so gwamnatin ta mayar da hankali a kai.
Gwamnan ya bayyana manyan bangarorin da aka fi ware kudi da suka haɗa da “ilimi naira biliyan 156.3, aiki da gidaje naira biliyan 117.1, noma naira biliyan 78.6, lafiya naira biliyan 67.5, albarkatun ruwa naira biliyan 62.8 da muhalli naira 53.8.
Hakan ya sanya ilimi ya zama fannin da aka fi warewa kudi, yayin da gwamnati ke ƙara zuba jari domin inganta makarantu da ingancin koyarwa.
Ya ce fiye da kashi 80 cikin 100 na kasafin kudin an ware shi ga aiyukan raya kasa musamman a fannonin gine-gine da ilimi da lafiya da ci gaban al’umma.
Gwamnan ya ce “hakan zai taimaka wajen samar da dama ga matasa da raya yankuna daban-daban da kuma ƙarfafa rayuwar jama’a a dukkan kananan hukumomin jihar.”
