Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, CON, ya tsallake rijiya da baya lokacin da da wasu mahara sanye da kayan sojoji suka kai wa tawagarsa hari.
Al’amarin ya faru ne a kusa da Babban Birnin Tarayya, Abuja, a ranar Lahadi 22 ga watan Oktoba, da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, yayin da Gwamnan ke ƙoƙarin komawa Lokoja don ya gabatar da wasu al’amuran gwamnati.
Kamar yadda wani rahoto daga fadar gwamnatin Kogin ya bayyana cewa, maharan sun buɗe wa ayarin motocin Gwamnan wuta, sai dai jami’an tsaron dake kula da Gwamnan sun yi nasarar ba su kariya.
An buƙaci mutane da su kai rahoton duk wani motsin da ba su yarda da shi ba ga jami’an tsaro, a yayin da Gwamnatin Kogin tace tana haɗa gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin kare al’ummar jihar.
