Home » Yahaya Bello Ya Ce Ba Hari Aka Kai Masa Ba

Yahaya Bello Ya Ce Ba Hari Aka Kai Masa Ba

by Halima Djimrao
0 comment

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya musanta labarin da ake yaɗawa cewa ya tsallake rijiya da baya, bayan da wasu ɓata gari suka kai masa hari da nufin daukar ransa.

Kwamishinan yaɗa labaran jihar Kogi Kingsley Fanwo ne ya sanar da cewa an kai wa gwamnan hari ranar Lahadi.

To sai dai Yahya Bello a hirarsa da manema labarai a Abuja, ya ce labarin da kwamishinan nasa ya faɗa ba haka yake ba, maimakon hakan ɗan wani akasi aka samu tsakanin tawagarsa da wata tawaga da suka gamu a hanya.

Ya ce rashin fahimta ne ya gilma tsakanin jami’an yan sandan dake tsaronsa, da kuma sojojin dake tsaron babbar hanyar da suka bi, wanda hakan ya haifar da saɓani, a ƙoƙarin da kowane ɓangare ya yi na neman tabbatar da tsaron da ya kamata.

Yahya Bello ya yi amfani da damar wajen yin kira ga mahukunta da su binciki takaddamar da ta faru tsakanin ɓangarorin biyu tare da ɗaukar matakin Ladabtarwa.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi