• Home  
  • Gwamnati ta sa dokar hana fita bayan ɓarkewar zanga-zanga a Neja
- Babban Labari

Gwamnati ta sa dokar hana fita bayan ɓarkewar zanga-zanga a Neja

Hukumomi a jihar Neja sun ƙaƙaba dokar hana fita a Minna, babban birnin jihar Neja sakamakon zanga-zangar da ta ɓarke. Mai bai wa gwamnan jihar shawara kan yaɗa labarai, Zayyanu A Salihu ya wallafa sanarwar a shafinsa na Instagram. Ya ce dokar ta tsawon sa’a 24 za ta soma aiki bayan sallar Juma’a. Hukumomi sun […]

Hukumomi a jihar Neja sun ƙaƙaba dokar hana fita a Minna, babban birnin jihar Neja sakamakon zanga-zangar da ta ɓarke.

Mai bai wa gwamnan jihar shawara kan yaɗa labarai, Zayyanu A Salihu ya wallafa sanarwar a shafinsa na Instagram.

Ya ce dokar ta tsawon sa’a 24 za ta soma aiki bayan sallar Juma’a.

Hukumomi sun shawarci jama’a da su mutunta dokar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai