Fannin ilimi a Jihar Jigawa na shirin samun gagarumin ci gaba, yayin da shirin Partnership for Learning for All in Nigeria (PLANE) ya ƙaddamar da sabon shirin horas da malamai kan koyar da harshen Ingilishi, wanda zai shafi malamai 337 na makarantun firamare daga makarantun 132 da aka zaɓa, lamarin da ake sa ran zai amfani ɗalibai sama da 30,000 daga ajin Firamare ɗaya zuwa uku.
Shirin ya biyo bayan kammala wani horo na kwanaki shida da aka yi wa manyan masu horaswa 26, wanda aka gudanar a Grand Amber Hotel da ke Jihar Jigawa.
Bayan kammala horon, ana sa ran fara sauke horon ga malamai a lokaci guda a ƙananan hukumomin da shirin PLANE ke aiki.
Ƙananan hukumomin sun haɗa da Dutse, Gagarawa, Jahun, Kafin Hausa, Malam Madori, Taura da Yankwashi.
Da yake jawabi kan shirin, Shugaban Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Jigawa (SUBEB), Farfesa Haruna Musa, ya bayyana tsoma bakin shirin PLANE a matsayin abin yabawa ƙwarai, musamman ta fuskar bunƙasa ƙwarewar malamai, samar da kayan koyo da kuma gina ƙwarewa a matakin ƙananan hukumomi.
Ya ce, “Gaskiya abin da shirin PLANE ke yi wajen horas da malamai, samar da kayan koyo da kuma gina ƙwarewa abin yabawa ne ƙwarai.”
Farfesa Musa ya bayyana cewa a baya shirin PLANE ya mayar da hankali kan amfani da harshen uwa wajen koyarwa a ƙananan azuzuwan firamare, wanda hakan ya haifar da sakamako mai kyau, musamman idan aka kwatanta da makarantun da ba su amfana da shirin ba.
Ya ƙara da cewa fara koyar da harshen Ingilishi daga ajin Firamare ɗaya zuwa uku wani muhimmin mataki ne a ci gaban ilimi.
“Fara koyar da Ingilishi tun da wuri zai taimaka wa yaranmu su kai matsayin duniya. Idan aka takaita koyo da harshen uwa kaɗai, ana rage damar yara su san Ingilishi da wuri,” in ji shi.
Shugaban na SUBEB ya jaddada buƙatar samar da isassun kayan koyarwa, inda ya buƙaci a samar da littafi guda ga kowane ɗalibi, ciki har da littattafan karatu, littattafan atisaye da jagororin malamai, domin cimma sakamako mai kyau a fannin koyo.
Farfesa Musa ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar na da ƙudirin koyon darasi daga tsarin PLANE domin samar da ingantaccen tsarin ilimi na cikin gida da zai dace da buƙatun Jihar Jigawa.
Ya ce, “Muna neman haɗin gwiwa da tallafi. Za mu yi nazari kan wannan shiri, mu koya daga gare shi, sannan mu samar da tsari da zai magance ƙalubalen da malamai ke fuskanta.”
Shi ma da yake jawabi, Mataimakin Shugaban Shirin PLANE na Ƙasa, Malam Samuel Achimugu, ya bayyana cewa shirin wani bangare ne na tallafin ilimi da Gwamnatin Birtaniya ke ɗaukar nauyi ta hannun Hukumar FCDO.
A cewarsa, shirin PLANE na aiki a jihohin Jigawa, Kano da Kaduna, domin inganta iya karatu da lissafi ta hanyar amfani da harshen da yara suka saba da shi, tare da ƙarfafa koyon harshen Ingilishi.
Ya ce, “Tun daga ƙirƙirar shirin, harshen gida da Ingilishi duka suna cikin tsarinmu. Da zarar an samu tallafin kuɗi, sai muka fara koyar da Ingilishi a matsayin harshe na biyu ga ɗaliban firamare ɗaya zuwa uku.”
Achimugu ya bayyana cewa wannan mataki na yanzu shiri ne na gwaji da ake aiwatarwa a makarantun sama da ɗari, inda ake sa ran faɗaɗa shi a duk faɗin jihar bisa sakamakon da za a samu tare da haɗin gwiwar gwamnatin Jigawa.
“Da zarar mun tabbatar cewa kayan koyarwar na aiki yadda ya kamata, za mu yi aiki tare da Ma’aikatar Ilimi da SUBEB domin faɗaɗa shirin a duk faɗin jihar,” in ji shi.
Ya kuma nuna jin daɗinsa kan yadda manyan masu horaswa da malamai ke gudanar da shirin, inda ya ce shirin zai taimaka wajen shirya ɗalibai yadda ya kamata kafin su koma koyarwa da Ingilishi a manyan azuzuwan firamare.
Shirin ya yi daidai da manufofin gwamnatin Jihar Jigawa na inganta sakamakon koyo da kuma shirya ɗalibai su iya fafatawa a matakin ƙasa da na duniya.
A nasa jawabin, Babban Mai Horaswa kuma Jagoran Taron, Abdullahi Yusuf, ya ce horon, wanda ke rana ta biyu, an shirya shi ne domin sauke sababbin dabarun koyarwa ga malamai na ajin Firamare ɗaya, biyu da uku a makarantun da aka zaɓa.
A cewarsa, wannan shi ne karo na farko da ake aiwatar da shirin a ƙarƙashin PLANE, inda aka fara da horas da manyan masu horaswa kafin a sauke shi zuwa matakin malamai domin faɗaɗa tasiri.
Ya ce, “Wannan horo zai ɗauki kwanaki shida, kuma duk abin da muka koya za mu sauke shi ga malamai daga makarantu daban-daban, domin ƙarfafa ingantacciyar koyarwa da koyo, musamman a harshen Ingilishi.”
Yusuf ya bayyana cewa mahalarta horon, waɗanda dukkansu malamai ne na Ingilishi, sun nuna ƙwazo da jajircewa tun daga ranar farko.
Ya ce, “Tun daga rana ta farko, malamai sun shiga ayyuka daban-daban, kuma yadda suke halartar horon da kuma yin atisaye abin ƙarfafa gwiwa ne.”
Ya ƙara da cewa an horas da malamai kan amfani da sabbin kayan koyarwa kamar flashcards, domin sauƙaƙa fahimtar darussa ga ɗalibai.
“Mun koya musu yadda ake ƙirƙira da amfani da flashcards wajen koyar da Ingilishi, kuma sun fara amfani da kwali da hotuna wajen yin atisaye,” in ji shi.
Yusuf ya kuma jaddada muhimmancin sauya harshe (code-switching), wato amfani da Hausa idan ya zama dole, domin tabbatar da cikakkiyar fahimta, musamman wajen bayanin darussa masu wahala.
Ya ce, “Wannan tsari zai kawo sauyi mai kyau a ilimin firamare, domin yana bai wa malamai damar yin bayani cikin sauƙi tare da bin ƙa’idojin koyarwa.”
Babban mai horaswar ya yabawa gwamnatin Jihar Jigawa bisa goyon bayan da take bai wa shirin PLANE, inda ya bayyana shirin a matsayin mai muhimmanci kuma wanda ya zo a kan lokaci.
- Ya ce, “Ina taya gwamnatin jihar murna da goyon bayan wannan shiri, domin ba wa malamai damar inganta ƙwarewarsu. Wannan zai taimaka ƙwarai wajen samar da ingantacciyar koyarwa da koyo a makarantun firamare.”
