• Home  
  • Gwamnatin Jihar Kano Ta Ƙuduri Aniyar Farfaɗo Makarantun Kimiya Da Fasaha
- Babban Labari - Labarai

Gwamnatin Jihar Kano Ta Ƙuduri Aniyar Farfaɗo Makarantun Kimiya Da Fasaha

Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada kuddirinta na farfaɗo da manyan makarantun kimiya da fasaha domin inganta harkokin koyo da koyarwa a fadin jihar.

Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada kuddirinta na farfaɗo da manyan makarantun kimiya da fasaha domin inganta harkokin koyo da koyarwa a fadin jihar.

Dokta Ibrahim Garba Muhammd ya bayyana ƙudurin gwamnatin ne yayin da Kwamitin Farfado Da Manyan Makarantun Ilimin Kimiya Da Fasaha suka Kai Ziyarar Gani da Ido, ga Daliban da Gwamnatin Jihar Kano ta Dauka domin Koya Masu Illimin Kimiya Da Fasaha.

Dokta Ibrahim Garba ya tabbatar da cewa an dauki nauyin ɗaliban ne domin su samu ilimin dogaro da kai, a Babbar Makarantar Kimiya Da Fasaha Ta Karamar Hukumar Kura.

Ya kara da cewa ziyarar duba daliban ta zo ne bisa umarnin da Gwamna Abba Kabir Yusif ya basu, na ganin sun tabbatar waɗanda aka zaba sun cimma nasara akan abinda suka koya, tare da basu tallafin kayan aiki idan sun kammala Karatun.

Babban Darakta a Makarantar Illimin Kimiya Da Fasaha da ke Karamar Hukumar Kura Alhaji Muutassin Uba Adamu ya bayyana cewa suna da tsari sosai na ganin ɗaliban sun samu abinda suke buƙata.

Kabiru Shitu Doguwa da Binta Sale Abubakar suna daga cikin ɗaliban da gwamnatin Kano ta ɗauki nauyin karatun su, bayyana farin cikin su da aniyar amfani da abin da aka koya musu.

Kwamatin dake kula da farfado da makarantun kimiya da fasahar na Kano, sun tabbatar da cewa akwai Makarantu 26 da Gwamnatin Kano zata gyara a fadin jihar domin dokar burinta na inganta rayuwar al’ummarta.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai