Gwamnatin Kaduna Ta Ce Shekaru 2 Da Rabi Ba A Samu Ricikin Addini Ko Kabilanci Ba

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ce an ɗauki tsawon shekara biyu da rabi ba tare da samun rikicin addini ko na ƙabilanci a jihar Kaduna ba.

Yayin da yake jawabi a wurin wani taro da cibiyar kula da al’amura ta duniya ta shirya ranar Talata a birnin Legas, gwamnan ya ce gwamnatinsa ta samu nasarar magance matsalar tsaro a jihar ta hanyar ɓullo da dabarun gwamnatin da ta haɗa kowa da kowa.

Jawabin gwamnan na zuwa ne makonni bayan da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi zargin cewa ana aikata kisan kiristoci a Najeriya, tare da yin barazanar ɗaukar matakin soji kan ƙasar.

Jihar Kaduna na daga cikin jihohin Najeriya da suka yi fice da rikicin addini da ƙabilanci a shekarun baya, kuma ta fuskanci hare-haren ƴanbindiga masu garkuwa da mutane.

Gwamna Uba Sani ya ce gwamnatin ta ɓullo da matakan masu yawa na ganin an magance matsalar tsaro a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *