Gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya amince da kashe Naira miliyan ɗari bakwai domin biya wa ɗalibai ‘yan asalin jihar nan su kusan dubu bakwai da ke karatu a jami’ar Bayero kudin makaranta.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ta shafukansa na sada zumunta na Fesbuk da X da aka fi sani da Twitter, inda ya ce sun yi wannan yunƙuri ne domin rage wa al’umma halin talauci da ake fama da shi.
Shi ma kwamishinan hukumar Manyan makarantu ta jihar, Dr Yusuf Kofar Mata, ya nuna rashin jin daɗinsa game da ƙarin kuɗin makaranta da wasu jami’o’i suka yi, sai dai ya ba da tabbacin gwamnatin jihar nan za ta cigaba da ƙoƙari wajen tallafa wa ɗaliban Kano.
A ƙarshe gwamnan jihar nan ya ce nan gaba kaɗan za su sanar da yadda tsarin biyan tallafin karatun zai gudana a hukumance.