Kotun daukaka kara, dake babban birnin tarayya Abuja ta kori karar da Abba Kabir Yusuf ya shigar na neman a yi watsi da hukuncin kotun Sauraren kararrakin zaben karkashin jagorancin mai shari’a Oluyemi Akintan Osadebay da ta zartar a ranar 13 ga Yuli, 2023.
Kotun ta yanke hukuncin ne a yau Alhamis, bayan ta bayyana karar da gwamnan Kano ya shigar a kan APC da wasu mutane 2 a matsayin “marar tushe, wadda da kuma ta cancanci a hukuncin kora”.
Izuwa yanzu dai ana daƙon ƙarin bayani game da wannan mataki da kotun ta ɗauka a kan wannan shari’a.