Home » Gwamnatin Najeriya ta sake kwaso ‘yan Kasarta 126 daga kasar Sudan saboda rikicin yaki

Gwamnatin Najeriya ta sake kwaso ‘yan Kasarta 126 daga kasar Sudan saboda rikicin yaki

by Anas Dansalma
0 comment
Gwamnatin Najeriya ta sake kwaso 'yan Kasarta 126 daga kasar Sudan saboda rikicin yaki

Gwamnatin Tarayya ta sake kwaso ‘yan Nijeriya 126 daga ƙasa Sudan sakamakon rikicin da ake yi a ƙasar tsakanin sojoji da rundunar RSF.

Mutanen da jirgin kamfanin Tarco ya ɗebo sun sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin ƙarfe 4:56 na yammacin jiya Asabar.

Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA, ita ce ta jagoranci ɗebo mutanen tare da haɗin gwiwar ma’aikatun harkokin waje da ta ‘yan Najeriya mazauna ƙetare, da sauransu.

Sai dai har yanzu akwai ɗaruruwan ‘yan Najeriyar da ke roƙon a kwaso su daga Sudan ɗin amma babu tabbas ko gwamnatin ƙasar za ta ci gaba da aikin kwashe su a yanzu.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi