Babban bankin Duniya ya amince da bukatar gwamnatin tarayya na cin bashin dala miliyan ɗari biyar, domin taimaka wa Najeriya a shirin tallafa wa mata.
Wannan shi ne bashi na biyu da bankin duniya ke amincewa da shi karkashin sabuwar gwamnati ta shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.