Mai Ba Wa Shugaban Ƙasa Shawara a Kan Harkar Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ya yi alƙawarin zage damtse don cika burin da ‘yan Najeriya ke da shi da kuma tabbatar da tsaron ƙasar daga duk wani nau’in rashin tsaro.
Malam Nuhu Ribadu ya yi wannan jawabibn ne yayi wata ganawa a Abuja in da ya bayyana nau’ikan tsaron kamar ayyukan ta’addanci da ‘yan fashin daji da satar mutane don neman kuɗin fansa da sauransu.