Gwamnatin Neja ta bukaci mazauna yankunan da suka gina gidaje a kan magudanan ruwa da su yi gaggawar tashi don kaucewa ambaliyar ruwa.
Mataimakin gwamnan jihar, Yakubu Garba ne, ya ba da umarnin a ranar Laraba, yayin ziyarar duba wasu yankuna da ambaliyar ruwa ta shafa, biyo bayan mamakon ruwan sama da aka yi a daren ranar Talata a Minna, babban birnin jihar.
Ya kuma umarci hukumar raya birane ta jihar da hukumar bada agajin gaggawa ta jihar (NSEMA) da hukumar kare muhalli ta jihar (NISEPA), da su wayar da kan jama’ar da ke zaune a magudanan ruwa domin su tashi.
Ya kuma ce ya ba hukumomin gwamnati da suka dace da su duba gidaje da gine-ginen da aka yi a kan hanyoyin ruwa sannan su tashi mazauna yankunan.
“Wannan wani mataki me kaucewa sake aukuwar ambaliyar ruwaa nan gaba,” a cewarsa.
Mataimakin gwamnan ya kuma shawarci jama’a da su guji sayen filaye a magudanan ruwa don kaucewa tafka asara.
Ya kuma gardadi jama’ar jihar da su daina zubar da shara a magudanan ruwa don hakan na haifar da ambaliyar ruwa.