30
Gwamnatin mulkin soji a jamhuriyar Nijar ta rusa ƙungiyoyin ƙwadago guda uku da ke wakiltar jami’an tsaro da suka haɗa da na ma’aikatan kwastam da na ma’aikatar kula da ruwa da gandun daji.
Wannan na ƙunshe cikin wata sanarwar da ma’aikatar harkokin cikin gida ta fitar.
Hukumomin sun ɗauki wannan mataki ne kamar yadda kundin tsarin mulkin na 26 ga watan Maris ɗin shekarar nan ya tanada.