A Najeriya, hukumar yaki da fataucin bil’adama ta NAPTIP ta kaddamar da wasu sabbin tsare-tsaren yaki da safarar mutane.
Ya yin wani taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya a Abuja, ta bayyana cewa a yanzu suna amfani da sabbin dabarun yaki da matsalar ciki har da manhajojin dijital, don samun bayanai.
Hukumar za ta kaddamar da shirye-shiryen wayar da kai da kuma kaddamar da jami’an tsaro masu yaki da fataucin mutane sama da 200.
NAPTIP ta sanar da cewa sun kubutar da fiye da mutum dubu bakwai wadanda aka yi yunkurin fita da su da kuma wadanda aka yi safararsu daga Najeriya.
Rahotanni sun ce matsalar safarar mutane na karuwa a sassan Najeriya,
Kungiyoyin da ke kare hakkin dan adam da kuma masu yaki da fataucin bil adama, na jaddada cewa akwai bukatar NAPTIP ta kara hada kai da jami’an tsaro da kungiyoyi da kuma hukumomin kula da shige da fice, sannan kuma gwamnati ta samar da yanayin da zai sa mutane su daina ficewa daga kasarsu da kuma tabbatar da cewa ana hukunta mutanen da ke safarar mutane don ya zama darasi ga masu niyyar aikata laifin.