Gwamnatin jihar Kano ta ce ta kammala tattara bayanan iyalan mutanen da aka kashe a Uromi da ke jihar Edo inda ta mika wa gwamnatin Edon sunayensu.
Tun da farko gwamnatin jihar ta Kano ta kafa kwamiti da zai gudanar da bincike tare da tattara bayanan iyalan mafarautan da aka kashe.
Mataimakin gwamnan jihar ta Kano ne ya jagoranci wata tawaga da suka je Edon inda suka mika rahoton da ke kunshe da bayanan.
Yayin mika rahoton, mataimakin gwamnan na Kano kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya fadawa gwamnan jihar Edo cewa,” Dama can mai girma gwamna na Edo kun mana alkawarin cewa za a yi wa mutanen da aka kashen adalci kuma mun yarda a kan hakan shi ya sa muka tattara bayanan iyalansu.Muna so ayi komai a bayyane cikin adalci wajen tabbatar da cewa an hukunta dukkan wadanda ke da hannu a kisan da aka yi wa mafarautanmu.”
A nasa bangaren, gwamnan jihar ta Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya da hadin gwiwar gwamnatin jihar Edo sun kafa kwamitin da zai binciko gaskiyar abin da ya faru a kan kisan da aka yi mafarauta a Uromi.
Gwamnan na Edo ya ce shugaba Bola Ahmed Tinubu, bai ji dadin abin da ya faru ba a Uromi sannan kuma ya kuduri aniyar tabbatar da cewa jihar da ma kasa baki daya za su zamo wurare masu aminci da kowa zai iya rayuwa da ma gudanar da kasuwanci.
Daga bisani gwamna Okpebholo da kuma tawagar Kano da ta je Edo sun ziyarci Uromi in da suka gana da al’ummar Hausawa da ke wajen.