Ministar Mata da Cigaban Al’Umma, Uju Kennedy-Ohanenye, ta ce gwamnatin tarayya ta haramta wa yara mata shiga kowanne irin otel a faɗin ƙasar nan.
Ministar ta bayyana hakan a Abuja yayin bikin yaye ɗalibai da suka ci gajiyar shirin da aka yi wa take da ‘Unlock training programme’ wanda mataimkiya ta musamman ga shugaban ƙasa kan sana’o’i da ilimin kasuwanci, Madam Abiola Arogundade.
Ministan ta ce wannan doka za ta fara aiki ne daga ranar 20 ga watan Yinin shekarar da muke ciki.