Gwamnatin Kano ta jaddada aniyarta na tabbatar da an bi dokar yin gwajin lafiya kafin aure wadda gwamnan ya sanya hannu a kanta.
A cikin ƙunshin dokar dai, an bayyana cewa za a ɗaura aure ne kawai idan an gabatar da shaidar gwajin lafiya sahihi da kuma ya ƙunshin gwajin da ke bayyana rukunin halittar mutum da a Turance ake kira genotype da gwajin cutar hanta nauyin B da C da cuta mai karya garkuwar jiki, HIV, da makamantansu.
Dokar ha’ila yau, ta tanadi hukuncin zaman gidan kaso na shekaru biyar ko tarar Naira dubu ɗari biyar ko duka biyun ga duk wanda ya karya dokar.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce wannan doka za ta tabbatar da haihuwar yara masu ingantaccen lafiya ta hanyar kuɓutar da su daga cututtuka da ake iya gadonsu.