Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci sabbin jami’an yan sandan da aka yaye, a jami’ar yan sanda dake garin Wudil Kano, su kasance masu riko da gaskiya da tare da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu.
Shugaban kasar wanda Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata Geoge Akume, ya wakilta ne ya bayyana hakan yayin gudanar da bikin yaye daliban yan sandan su dubu daya da dari da tamanin da bakwai (1187).
Shugaban kasar , ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na ƙoƙari sosai , wajen inganta harkar tsaro a fadin Nijeriya.
Haka zalika, ya yaba wa makarantar, bisa yadda take jajircewa a koda yaushe na samun kwararrun dakaru wadanda suke fitar da Nijeriya kunya.
Sanata Akume, ya ce bikin yaye daliban wani muhimmin al’amari ne duba da yadda ake fama da matsalar tsaro a wasu sassan Nijeriya, inda ya ce hakika za su bayar da gudunmawa sosai don tabbatar da tsaro da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu, bisa horon da suka samu daga makarantar.
Shugaban Ƙasar ya ja kunnen sabbin jami’an da su kasance masu gaskiya da adalci.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa makarantar ‘yan sandan da sauran hukumomin tsaro ta hanyar samar da horo da kayan aiki, da sauran muhimman abubuwa.
A nasa jawabin, Kwamandan makarantar, AIG Patrick Adedeji Atayero, ya ce dukkan sabbin jami’an sun kammala karatunsu da samun horo, inda suka samu digiri a fannoni daban-daban.
Ya kuma yabawa sabbin jami’an saboda biyayyarsu da nuna kwarewa da hakuri yayin da suke karbar horo da darussan makarantar.
Taron ya samu halattar babban sufeton yan sandan Nijeriya, IGP Kayode Adeolu da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da shugabannin hukumomin tsaro, yan majalissu, sarakunan gargajiya da iyaye da sauran al’umma daga sassa dabam-daban na Nijeriya.

