• Home  
  • Gwamnonin Najeriya Za Su Gana da Hukumomin Tattalin Arziƙin Ƙasar
- Labarai

Gwamnonin Najeriya Za Su Gana da Hukumomin Tattalin Arziƙin Ƙasar

Gwamnonin Jihohi 36 na Tarayyar Nijeriya za su gana da dukkan hukumomin tattalin arziki da masu samar da kudade na kasar nan, da nufin kawar da matsalolin da suka dabaibaye tsaron jihohinsu

Gwamnonin Jihohi 36 na Tarayyar Nijeriya za su gana da dukkan hukumomin tattalin arziki da masu samar da kudade na kasar nan, da nufin kawar da matsalolin da suka dabaibaye tsaron jihohinsu, wajen samar da ingantacciyar hanyar sarrafa kudade.

Taron wanda zai gudana a ranar Talata 4 ga watan Afrilu, bisa ga gayyatar da Darakta-Janar na ƙungiyar gwamnonin Nijeriya, Mista Asishana Bayo Okauru, ya bayar, domin tabbatar da halartar dukkan masu ruwa da tsaki cikin lamarin.

A cewar sanarwar da daraktan yada labaran kungiyar, Abdularaque Bello Barkindo, ya ce wadanda aka gayyata zuwa taron sun hada da EFCC, ICPC, Hukumar Kula da Harajin Cikin Gida ta Tarayya (FIRS) da Babban Bankin Nijeriya (CBN).

Bugu da kari, ya ce taron zai kuma yi la’akari da zurfafa gudanarwa da fadada manufofin rashin kudi wanda ya fara aiki tun daga lokacin da aka sauya fasalin kudin kasar nan, a shekarar da ta gabata.

Ya ce, Wannan taron an shirya shi ne domin nemo mafita kan matsalolin kudi.

Yace za’a shawarci dukkan gwamnoni da su bai wa taron fifiko don tattauna abubuwan da ke da nasaba da taron.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai