Home » Gwmnatin Kano bayyana dalilanta na sakale hoton sarkin Kano Sunusi II

Gwmnatin Kano bayyana dalilanta na sakale hoton sarkin Kano Sunusi II

by Anas Dansalma
0 comment
Gwmnatin Kano bayyana dalilanta na sakale hoton sarkin Kano Sunusi II

Tun a jiya ne aka fara cecekuce game da saƙele hoton sarki Kano na 14, Muhammad Sunusi II a ɗakin taron gidan gwamnatin jihar Kano da aka fi sani da Coronation Hall.

Tuni dai al’umma suka fara kallon hakan a matsayin wata ‘yar manuniya ta sake dawo da sarkin kan karagarsa ta sarautar Kano.

Sai dai Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana cewa a sanin sa babu wani yunƙuri na dawo da sarkin Kano na 14 kan karagar Sarautar Kano.

Ya kuma ƙara da cewa zauren Coronation zauren ne wanda a cikin sa aka mika shaidar kama aiki ga sarki Muhammad Sanusi II bayan ya gaji marigayi Alhaji Ado Bayero a shekarar 2014 a lokacin gwamnatin Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso.

A yanzu haka ana ci gaba da gyare-gyarensa ne domin dawo da martabar dakin taron mai ɗimbin tarihi dake fadar gwamnatin jihar nan.

Sannan ya bayyana cewa wani muhimmin abu game da wannan aikin na gyare-gyare shi ne mayar da hoton Sarki na 14, Malam Muhammadu Sanusi, a cikin zauren wanda saboda da shi ne aka gina dakin.

Domin haka hotonsa zai kasance a saƙale har abada, donmin tunawa da sarautar tsohon sarki.

Ya kuma ce zauren taro na Coronation yana da kima sosai ga al’ummar Kano, kuma gyaran da aka yi masa na nuna aniyar gwamnatin na kiyaye dimbin tarihi da al’adun gargajiya na mutanen Kano.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi