RAHOTO: Hassan Umar Shamfella, Adamawa.
Gwamnatin jihar Adamawa ƙarƙashin jagorancin Ahmadu Umaru Fintiri, ta saka dokar hana fita ta tsawon awowi 24, a faɗin jihar, biyo bayan farfasa wuraren ajiyar abinci da matasa suka yi.
Mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan jihar Adamawa ya ƙara da cewa i zuwa yanzu an kama mutane 44, kuma an ƙwato sauran kayayyakin da aka sace.
Har wa yau kuma mun jiyo ra’ayoyin wasu mazauna garin na Yola dangane da wannan al’amari da ya faru.