Home » Shugaban Najeriya ya amince da shirin siya wa kungiyoyin dalibai motocin bas

Shugaban Najeriya ya amince da shirin siya wa kungiyoyin dalibai motocin bas

by Anas Dansalma
0 comment
Shugaban kasar Najeriya ya amince da shirin siya wa kungiyoyin dalibai motocin bas

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya amince da batun saya wa ƙungiyoyin ɗaliban dukkan jami’o’in da kwalejojin ilimi dake faɗin ƙasar nan motocin bas.

Mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan ayyuka na musamman, Dele Alake, ne ya bayyana hakan a cikin wani jawabi da ya yi a yau.

Ya ce wannan na cikin yunkurin da shugaban ƙasa ke yi ne na rage raɗaɗin cire tallafin mai ga ɗaliban da ke manyan makarantu a faɗin ƙasar nan.

Ya ce shirin zai taimaka wajen saukaka wa dalibai samun damar zuwa makarantunsu cikin sauki ba tare da shan wahala ba game da zirga-zirga.

Sannan ya ce hakan zai rage wa iyaye kudin da suke ba wa ɗalibai domin zuwa makaranta wanda hakan ke nufin ba za su damu ba game janye tallafin man ba da gwamnati ta yi.

Hadimin shugaban ƙasar ya kuma tabbatar da cewa shugaban  ƙasar ya amince da cire dukkan ƙa’idojin da aka sa na ba da bashin kudin karatu ga dalibai.

Wannan wani yunkuri ne shi ma na tabbatar da cewa kowanne dalibi a Najeriya ya samu damar samun rancen kudin.

A ƙarshe, shugaban ƙasar ya ja kunnen makarantu game da ƙara kudin makaranta na ba gaira ba dalili.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi