Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin kai kayan agaji da taimakon da ya wajaba nan take ga mutanen da suka kuɓuta da kuma dangi da iyalan waɗanda suka mutu a hatsarin jirgin ruwan Kwara.
Wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na shugaban ƙasa Abiodun Oladunjoye ya fitar, ta ce, shugaban ƙasa ya nuna takaicin wannan hatsarin jirgin ruwa da ya kashe mutum 150 a jihar ta Kwara.
Ya kuma umarci gwamnatin jihar Kwara da sauran hukumomin gwamnatin tarayya da lamarin ya shafa su yi aiki tare don gano sanadi na kusa da na nesa da suka janyo aukuwar hatsarin jirgin ruwan.
Shugaban ya kuma yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta yi nazari kan matsalolin sufurin ruwa a ƙasar nan, don tabbatar da ganin ana aiki da matakan kare rayuka da ƙa’idojinsu.