Majiyarmu ta ruwaito cewa Mallam Yusuf Abubakar Hayat, sakataren masarautar ya sanar da wannan mataki a cikin wata sanarwa da ya
Ya ce matakin ya zo ne bayan tafiyar da Mai martaba Sarkin Zazzau Mallam Ahmed Nuhu Bamalli ya yi zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana.
Sanarwar ta kara da cewa, Sarkin wanda tuni ya taya al’ummar masarautarsa ta Zazzau murnar barka da sallah,
ya kuma yi kira ga daukacin al’ummar Najeriya su gudanar da addu’o’i don samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.
Ana shafe tsawon kwana uku ana hawan dawaki a Masarautar ta Zazzau duk shekara, a wani ɓangaren na bikin babbar salla.