• Home  
  • Najeriya ta doke Iran da ci 2 a wasan sada zumunta
- Babban Labari

Najeriya ta doke Iran da ci 2 a wasan sada zumunta

Tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Super Eagles, ta doke ƙasar Iran da ci 2 da 1 da wasan sada zumunta da suka buga a ranar Juma’a. Ƙasashen biyu sun kara da juna a filin wasa na Mardan Sport Complex da ke yankin Antalya na ƙasar Turkiyya. Ɗan wasan gaban Super Eagles, Moses Simon ne ya […]

Tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Super Eagles, ta doke ƙasar Iran da ci 2 da 1 da wasan sada zumunta da suka buga a ranar Juma’a.

Ƙasashen biyu sun kara da juna a filin wasa na Mardan Sport Complex da ke yankin Antalya na ƙasar Turkiyya.

Ɗan wasan gaban Super Eagles, Moses Simon ne ya fara jefa ƙwallo a raga a minti 6 da fara wasan.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Akor Adams ya jefa wa Najeriya ƙwallo ta biyu a raga a minti ma 51.

Shi kuma ɗan wasan gaban ƙasar Iran Mehdi Taremi ya jefa wa ƙasarsa ƙwallo a raga.

’Yan wasan Super Eagles, Samuel Chekwueze da Ademola Lookman ne suka taimaka wajen jefa wa Super Eagles ƙwallaye biyu a raga.

Fitaccen ɗan wasan gaban Super Eagles, Victor Osimhen bai samu buga wasan ba sakamakon raunin da ya samu a hannunsa a wasan da Galatasaray ta yi da Liverpool a Gasar Zakarun Turai.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai