Home » Hayakin gobarar daji na cigaba da yi wa ƙasar Canada da Amurka barazana

Hayakin gobarar daji na cigaba da yi wa ƙasar Canada da Amurka barazana

by Anas Dansalma
0 comment
Rahotanni a jiya na nuna cewa hayakin da ke fitowa daga gobarar daji a kasar Canada ya kwarara har zuwa Gabashi da Yammacin tsakiyar Amurka, inda ya mamaye manyan biranen kasashen biyu a cikin wani yanayi mai muni.

Rahotanni a jiya na nuna cewa hayakin da ke fitowa daga gobarar daji a kasar Canada ya kwarara har zuwa Gabashi da Yammacin tsakiyar Amurka, inda ya mamaye manyan biranen kasashen biyu a cikin wani yanayi mai muni.

Ya kuma hana jiragen sama tashi a manyan filayen jirgin sama, da dage wasannin kwallon Baseball inda kuma mutane suka koma sanya takunkumin rufe fuska kamar a lokacin annobar COVIDD-19.

Firefighters stand on a Kamloops Fire Rescue truck at a wildfire near Fort St. John, British Columbia, Canada May 14, 2023. Kamloops Fire Rescue/Handout via REUTERS THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. NO RESALES. NO ARCHIVES

Jami’an Canada sun nemi karin taimako daga wasu kasashe domin yaki da harsunan wuta fiye da 400 da ke ci a fadin kasar da tuni suka raba mutane 20,000 da muhallansu.

Gurbatacciyar iska mai haɗari ta bazu ne zuwa yankin birni New York, da wasu sassan Pennsylvania da New Jersey da ma Arewacin jihohin Carolina da Indiana, wanda hakan ya shafi rayukan miliyoyin mutane.

Jami’an Canada sun ce lamarin na rikidewa zuwa gobarar daji mafi muni da aka taba samu a kasar. Ta fara ne da farko a kan busasshiyar ƙasa fiye da yadda aka saba kuma ta yi saurin bazuwa sosai, ta karar da kayayyakin kashe gobara a duk faɗin ƙasar, da kuma gajiyar da masu kashe gobarar, in ji jami’an kashe gobara da muhalli.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi