Hisbah ta Jihar Kano ta tarwatsa wani taro da ake zargin ya shafi auren jinsi a wani dakin taro da ke unguwar Hotoro By-pass a cikin birnin Kano, a ranar Asabar, 25 ga Oktoba, 2025.
Rahotanni sun ce taron, wanda aka gudanar a Fatima Event Center, ya jawo hankalin jami’an Hisbah bayan samun bayanan sirri daga wasu mazauna yankin.
Mukadashin babban kwamandan Hisba a bangaren ayyuka na musamman Dr Mujahedeen Aminuddeñ Abubakar shi ne ya bayyana ga manema labarai.
Dakta Mujahideen ya ce jami’an Hisbah sun isa wurin ne inda suka tarwatsa taron tare da kama mutane 25 Wadanda suka hada da maza 18 da kuma mata 7 waɗanda ake zargi da hannu a lamarin.
Wadanda ake zargin sun hada da Abubakar Idris, a matsayin Ango da Aliyu Abdullahi da Adamu Ali da Umar Haruna da Abdulkadir Hassan da Ibrahim AbubaKar da Aminu Umar da Yusuf Muktar da Adam Muhammad da Shuaib Musa da Bashir Ismail da Bashir Shuaibu da Abba Musa da Aliyu Sulaiman da Sabo Alhaji da Abba Rabiu da Nasiru Ali da kuma Sulaiman Umar Usman.
Matan kuma sun hada da Rukayya Isyaku da Rabi Abdul Hamid da Amina Usman da Fatima AbubaKar da Khadija Usman da Sadiya Abdullahi da Halimatu Sani.
Dr. Mujahideen ya ce dukkan matasan Yan Jihar Kano ne daga suka fito daga mabambantan unguwanni.