Fadar shugaban Nijeriya ta yi fatali da wani rahoto da kungiyar Tarayyar Turai, EU, ta fitar da ke nuni da cewa akwai kura-kurai a zaben kasar nan da aka yi na 2023.
An gudanar da zaben shugaban kasar ne a watan Fabrairu inda hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya, INEC, ta ayyana dan takarar jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara.
A rahoton da jagoran kungiyar Tarayyar Turai Barry Andrews ya fitar ya ce an tafka kura-kurai a zaben don haka ba shi da sahihancin da ya kamata.
Inda a wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Mr Dele Alake ya fitar a jiya, ya yi watsi da rahoton na kungiyar Tarayyar Turan tare da zargin ta da nuna son kai karara.
Mr. Alake ya ce da ma tun a watan Mayu suka sanar da ‘yan Nijeriya cewa wata kungiya na shirin fitar da rahoto da zummar bayyana zaben kasar a matsayin gurbatacce.
Kungiyar dai ta ayyana rahoton a matsayin rahotanta na karshe, inda Alake ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da duniya cewa muna sane da tuggun Tarayyar Turai na jaddada son kai da ikirarinta mara tushe kan sakamakon zaben.
Ya kara da cewa abin takaici ne yadda Tarayyar Turai, wadda ta tura masu sanya ido da ba su kai 50 ba a kasa mai akwatunan zabe fiye da 176,000, ta fito tana cewa zaben kasar bai inganta ba.
Ya kuma ce yana so su san ta yaya EU ta hada rahotonta na karshe bayan kuwa masu sanya idanunta a zaben kalilan ne wadanda, babu shakka, sun dogara ne da jita-jita da masu sharhi a soshiyal midiya da ba su da masaniya da kuma masu magana da yawun ‘yan hamayya wajen hada rahoton nasu.