Hukumar HISBAH ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa sun gano waɗan da suke ɗaukar nauyin yaɗa biyon tsiraici da ke tashe a ‘yan kwanakin nan,
Shugaban Hukumar a Jihar Kano, Mallam Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayyana hakan , inda yace a binciken da suka gudanar, sun gano cewa daga ƙasashen waje ake ɗaukar nauyin masu yin waɗannan bidiyo kuma su yaɗa shi a kafafen sada zumunta.
A satin da ya gabata ta ne dai ake zargin wata budurwa da sakin faifan bidiyon ta tsirara har na tsawon mintuna uku, babu ko zani a jikin ta.
Bayyanar wannan bidiyo ya haifar da cece-kuce a tasakanin mabiya shafukan na sada zumunta.