Mamallakin matatar mai ta Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya ce lokaci ya yi da ya kamata gwamnatin tarayya ta kawo ƙarshen biyan kuɗin tallafin mai.
A wata ganawa da manema labarai da hamshaƙin ɗan kasuwar yayi ranar Litinin, ya ce tallafin man zai sa gwamnatin ta riƙa biyan kuɗin da bai kamata ta biya ba.
Ɗangote ya ƙara da cewa shugaba Tinubu ba zai iya cigaba da biyan kuɗin tallafin ba.
Tun a ranar da aka rantsar da Shugaba Tinubu ne dai ya ayyana soke biyan kuɗin tallafin man fetur ɗin. To sai dai ana zargin gwamnatin tarayya na cigaba da biyan kuɗin ta bayan fage.
Aliko Ɗangote ya bada wannan shawarar ne bayan da matatarsa ta fara dakon tattaccen man fetur ɗin akan kuɗi Naira 950 a duk lita a Jihar Legas, da kuma Naira 1,000 a wasu jihohin Arewacin Najeriya.
Ƴan Najeriya sun shiga wahala ne dai tun bayan da gwamnatin Najeriya ta ayyana janye tallafin man fetur ɗin baki ɗaya, hakan ya haifar da hauhawar farashin kayan masarufi wanda baya rasa nasaba da janye talllafin.
To bayan ƙaddamar da matatar man fetur ta Ɗangote, da yawa daga cikin yan ƙasar ke fatan za’a samu sauƙi na farashi dama samuwar man fetur ɗin, to sai dai har zuwa yanzu wannnan sauƙi bai samu ba.Masana tattalin arziki dai sun rabu akan mahimmancin ko rashin cire tallafin, inda wasu suke ganin cire tallafin shine mafita wasu kuma ke ganin hakan bazai haifar da ɗa mai ido ba.