• Home  
  • Hon. Idris Ɗankawu ya yi alƙawarin ci gaba da ayyukan raya ƙasa da sana’o’in dogaro dakai a Kumbotso
- Babban Labari

Hon. Idris Ɗankawu ya yi alƙawarin ci gaba da ayyukan raya ƙasa da sana’o’in dogaro dakai a Kumbotso

Ɗan majalissar tarayya dake wakiltar ƙaramar hukumar Kumbotso, Hon Idris Ɗankawu, ya bayyana cewa za su ci gaba da himdawa al’umma ta kowacce fuska tare da gabatar da aiyukan raya ƙasa kamar yadda ya saba. Ɗan majalissar ya bayyana hakanne a wani saƙo da wallafa a shafinsa na facebook, inda ya ce yanzu haka suna […]

Ɗan majalissar tarayya dake wakiltar ƙaramar hukumar Kumbotso, Hon Idris Ɗankawu, ya bayyana cewa za su ci gaba da himdawa al’umma ta kowacce fuska tare da gabatar da aiyukan raya ƙasa kamar yadda ya saba.

Ɗan majalissar ya bayyana hakanne a wani saƙo da wallafa a shafinsa na facebook, inda ya ce yanzu haka suna dakon karɓar haƙƙoƙinsu na aikace-aikacen mazaɓu na majalissa ( constituency project fund) na shekarar 2025.

Ya ƙara da cewa za a ƙarasa aiyukan raya ƙasa da aka faro su, tuntuni, a wasu daga cikin mazaɓu haɗi da ƙaddamar da sababbi.

Hon. Dankawu, ya jaddada cewa zai ci gaba da amfani da damar da yake hannunsa don jiƙa hantar ƴaƴan jam’iyyar da ababen hawa da kuma bayar da da tallafin jari don dogaro da kai a faɗin ƙaramar hukumar Kumbotso dake jihar Kano.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai