Home » Sanatan Kaduna Ya Tsallake Rijiya Da Baya

Sanatan Kaduna Ya Tsallake Rijiya Da Baya

by Mubarak Ibrahim Mandawari
0 comment

Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Lawal Usman Adamu, ya tsallake rijiya da baya a wani hari da ’yan ina-da-kisa suka kai masa.

Sanatan, wanda aka fi sani da Mista La, ya sanar da haka ne a cikin dare, jim kaɗan bayan faruwar lamarin.

Daga da ƙarfe 10 na daren ranar Laraba ne Mista La ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa Allah Ya yi masa gyadar dogo bayan harin neman kashe shi da ka yi.

Dazun nan na tsallake rijiya da baya a wani harin neman kashe ni da aka yi a yankin Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa,” in ji Sanatan.
Sanarwar tasa ke da wuya mutane suka fara tsokaci a kai.

A yayin da wasu jajantawa suke wasu kuma  taya shi murnar samun kuɓuta suke, wasu kuma sun ƙara nuna damuwa kan taɓarɓarewar sha’anin tsaro.

Wasu kuma sun bayyana damuwa cewa idan har babban mutum kamarsa zai shiga irin wannan yanayi, to ina ga talaka.

Sanata Lawal Usman Adamu shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawa kan ilimin bai-ɗaya a matakin farko.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?