Babban Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Yusuf Lawan, ya danganta nasarar da jihar ta samu a aikin hajjin bana ga gudunmawa da jagorancin Gwamnan Kano ABBA Kabir Yusuf.
A cewarsa jagororin hukumar da suka gabata sun damalmala al’amuran aikin hajji a hukumar,
Ya ƙara da cewa, da ba don ɗaukin da suka samu daga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ba, da ba su iya gudunar da ayyukan kamar yadda aka gani ba.
Alhaji Yusuf Lawan ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai a birnin MAKKA.
Ya ce an ba wa jihar Kano kujerun aikin hajji 6,105, amma jami’an hukumar ta jin dadin alhazan da suka gabata, sun siyar da ƙarin kujeru 191, waɗanda har yanzu ba a gano inda kuɗin ƙarin kujerun suka shiga ba.