Hukumar kare bayanan sirrin masu amfani da intanet ta ƙasa (NDPC), ta ce umarnin da Babban Bankin Ƙasa (CBN) ya bai wa bankuna na neman bayanan soshiyal midiya na abokan hulɗarsu ya saɓa doka.
A ranar 26 ga Yuni ne CBN ya umarci bankuna da su riƙa karɓar bayanan soshiyal midiya na abokan hulɗarsu domin ƙara samun cikakkun bayanai game da su.
CBN ya ce hakan zai taimaka wurin yaƙi da halatta kuɗaɗen haram da kuma hada-hadar ta’addanci.
Sai dai a wata sanarwa da hukumar NDPC ta fitar ranar Alhamis ɗin nan ta ce ta na tattaunawa da CBN game da sanarwar.