Hukumar NDLEA mai yaki da safarar miyagun kwayoyi ta tabbatar wa masu neman aiki da ita cewa suna kokarin magance matsalolin da ake fuskanta.
An shafin internet ɗin da masu sha’awar aiki da hukumar ta NDLEA za iya shiga don su nema, sai dai masu neman aikin na fuskantar tasgaro wajen cikewa kamar yadda aka tabbatar a makon nan.
Hukumar tarayyar ta fitar da wata sanarwa ta bakin Kakakin hukumar NDLEA na kasa, Femi Babafemi ya ce ana magance matsalar da aka samu wajen neman aiki.
Da yake magana a ranar Laraba, Femi Babafemi ya ce tun a ranar Talatar nan hukumar ta bunkasa fasaharta ta yadda mutane 53, 170 suka nemi gurabe.
ya ce an dauki matakin ne bayan mutane sun yi wa shafin yawa a ranar Lahadi da aka fara shirin daukar aikin.
A lokaci guda aka samu sama da mutane fiye da 200, 000 da suke neman yadda za su shiga shafin.
Babafemi a madadin hukumar ta NDLEA ya nemi afuwar wadanda suka yi yunkurin neman aikin ba tare da nasara ba, ya ce an kawo karshen matsalar a yanzu.
Sanarwar da aka fitar a makon nan, ta kara da kira ga masu sha’awar aiki da hukumar su yi hakuri.