Da sunan Allah mai girma, tsira da amincin Sa su tabbata ga farin jakada da iyalin sa, da sahabban sa da wadanda suka bisu da kyautatatawa har zuwa ranar lahira.
Bayan haka, a yau bayanin mu zai kalli hukumar haqowa, tacewa da sayar da man fetur ta kasa, wato NNPC.
Sanin kowa ne cewa wannan ma’aikata an kafa ta ne shekaru da yawa da suka wuce, bayan gano dimbin arzikin danyen mai da Allah ta’ala Ya baiwa kasar nan. Daga lokacin kafa ta zuwa wasu shekaru a baya, ma’aikatar tayi rawar gani wajen tabbatar da samuwar nau’in mai kamar fetur, kananzir, disel, man jirgi da sauran su. Wanda wannan na daga sanadin bunkasar tattalin arzikin Najeriya. Kafin wannan lokaci, tattalin arzikin Najeriyar ya damfara ne da noma da kiwo. Daga lokacin mulkin mallaka na turawan Ingila, har zuwa samun ‘yancin kai a shekarar 1960, kudaden gudanar da al’amuran mulkin kasa yana samuwa ne ta hanyar noma da harajin da ake karba a hannun ‘yan kasa.
Mu dauki misali, arewacin Najeriya su ke da yawan jama’a da wadatattun filyen (gonaki) noma. Sannan ga arzikin dabbobi kamar shanu, tumaki, akuyoyi da sauran su.
Wadannan albarkatu sune aka dinga sarrafawa, ana samun kudin tafikar da al’amuran kasa. A sassan Katsina da Kaduna, auduga ta zama babbar amfanin gona da ake nomawa. A Kano ta lokacin kuma wanda ta hada Jihohin Kano da Jigawa a yau, gyada ce babban amfanin gona da aka fi shukawa, bayan gero da dawa. Wannan tasa a Kano ake da filin dalar gyada a kofar mazugal da Nassarawa. Daga nan ne ake lodin gyadar zuwa sassa daban-daban na duniya ta hanyar jirgin kasa zuwa Legas daga nan kuma a dauka a jirgin ruwa zuwa kasashen turai.
Hakanan, kiraga da fatun dabbobi daga wannan yanki, ake daukar su zuwa kasashen ketare don sarrafa su zuwa takalma, jakankuna, bel da sauran su.
Haka abin ya kasance har aka gano albarkatun mai a kasar. Amma kash !! samun man sai ya kautad da harkar noma da kiwo a idanun shugabbani. Rangwame (subsidy) da ake bawa manoma sai ya fara yin kasa.
Ba shakka Najeriya tayi kawaye a duniya, kuma ta samu arzikin kudi mai yawa sanadin man fetur din nan. Kuma a lokacin an yi amfani da kudin wajen gina kasar, kamar ma’aikatu, masana’antu, makarantu, gidaje, tituna da sauran su.
Ana tafe yau da gobe, sai kasa ta fara shiga wani yanayi, sakamakon son zuciya da wasu yan’kasa musamman jami’an gwamnati suka tsunduma ciki.
Ya kasance a Najeriya muna da matatun mai guda hudu (Fatakwal, wari, Legas da Kaduna,) wadanda su ke tace mai sannan a raba shi a cikin kasa, da kuma safarar sa zuwa kasashen waje. Amma a dalilin wancan son zuciya, aka wayi gari duk matatun nan suka tsaya, suka daina aiki. Tun daga lokacin yan’najeriya, muka shiga rudani. Kasancewar man fetur na da alaka da kusan kowane lamari a cikin kasa.
A yanzu an dau shekaru masu yawa a cikin wannan hali, har ta kai don lalacewa wai sai an dau danyen mai a Najeriya, zuwa wasu kasashe an tace, sannan a dawo da shi. Wanan tasa farashin sa ya dinga tashi lokaci zuwa lokaci. Kwaram, bayan zuwan gwamnati mai ci ta Bola Tinubu sai ta janye tallafin safarar man. Wannan ya dada jefa rayuwar dan Najeriya cikin tsanani sosai.
To yanzu dai an ji a kafafen yada labarai cewa matatar mai ta Fatakwal ta dawo aiki. In dai labarin ya inganta ba farfagandar gwamnati ba ce, lallai ne mu gode Allah madaukaki. Sannan mu godewa gwamnati tare da fatan Allah Ya basu ikon gyara sauran ma. Tsammanin hakan zai taimaka wajen samun sassaucin rayuwa in Allah Ya so. Haka kuma kokarin kafa matatar mai da babban dan kasuwa, Aliko Dangote yayi, da kuma yunkurin da aka ce shima Abdussamad Isyaka Rabi’u (BUA Group) yake yi don samar da tasa matatar, abun a yaba ne. Allah ta’ala Ya wuce gaba.
A karshe ina fata Allah ta’ala Ya dube mu da idon rahama, Ya kawo mana karshen tashe-tashen hankula da halin kunci da ya addabi kasar mu, musamman arewacin najeriya.
Muhammad S. Ahmad
Bayero University Kano
27/ 11/ 24